Zaben Kogi: PDP zata fara yakin neman zaben ta

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta fara yakin neman zaben na gwamnan jahar Kogi a ranar Juma’a 25 ga watan Oktoba 2019.

Saidai kuma jam’iyyar PDP tace ta gano wani makirci na jam’iyyar APC da gwamnan jahar ta Kogi Yahaya Bello ke shiryawa wajen ganin sun dakile yakin neman nasu, inda kakakin jam’iyyar, Kola Ologbodiyan ya ce mambobin PDP da magoya bayanta su gama shirin su tsaf wajen daukar mataikai, da kuma tunkarar APC da Yahaya Bello wajen yukurin na hanasu gudanar sa shirin nasu.

Tuni dai PDP nada kaso 70 na masu zabe da aka yiwa rijista a kananan hukumomi 18 cikin 20 da ka jahar ta Kogi, a cewar kakakin na jam’iyyar PDP

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More