Zaben Kogi: Yadda jam’iyyar PDP zata tsayar da dan takarar ta a Kogi

Jam’iyyar PDP ta ce wakilai 2,578 ne a ke sa ran za su zabi dan takarar gwamnan da jam’iyyar za ta tsayar a zaben gwamna da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwambar wannan shekara a jihar Kogi.

A yau Talata 3 ga wata setemba 2019,  jam’iyyar ta PDP za ta gudanar da zaben fidda gwanin a Lokoja wato  babban birnin Jahar ta Kogi.

Sakataren watsa labarai na jam’iyyar a Jahar Kogi, Bode Ogunmola,  ya tabbatar da hakan a yayin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin . Ya ce, jam’iyyar ta shirya tsaf, don gudanar da sahihin zaben fidda gwani mai tsafta, wanda zai samu karbuwa ga dukkan ’yan takarar gwamnan.

A ranar Alhamis 28 ga watan Agusta ne  jam’iyyar APC  ta gudanar da nata zaben fidda gwanin, inda Gwamna Yahaya Bello ya lashe zaben da rata mai yawa kuma a yanzu shi ne dan takarar gwamnan da jam’iyyar ta tsayar kuma zai fafata da sauran ’yan takara da jam’iyyu daban-daban za su tsayar da su a matsayin  yan takara gwamna a zaben da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba  2019.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More