Zaben Kogi: Za’a dama da Natasha ta jam’iyyar SDP

Kotu ta bayyana cewa ba daidai bani cire yar takarar gwamnan jahar Kogi ta karkashin jam’iyyar SDP wato Natasha Akpoti daga jerin yan takarkarun da INEC tayi.

A zaman na yau Alhamis 7 ga watan Nuwamba 2019, kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta saka sunanayen yar takarar gwamnan jahar Kogi na karkashin jam’iyyar SDP tare da maitaimakin ta cikin jerin sunayen yan takarkarun zaben gwamnan wanda za’a gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba 2019.

Hakkan ya nuna cewa za’a dama da Natsaha a zaben dake gabatowa na jahar ta Kogi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More