Zaben Zamfara: Kotun kolin Najeriya ta sake dage zaman sauraren karar

Kotun kolin Najeriya ta sake dage zaman sauraron karar da jam’iyyar All Progressives Congress APC ta shigar, domin sake yin duba  gama da hukucin da kotun ta yanke na ranar 24 ga Mayun 2019, wanda ta kwace dukkan kujerun da yan takarkarun da suka lashe zaben a karkashin jam’iyyar APC kuma tabawa jam’iyyar PDP na jahar Zamfara.

Hakkan ya afku ne bisa dalilin rashin gudanar da zaben fidda gwani da APC tayi, wanda ya bawa gwamna Bello Matawalle na jam’iyyar PDP damar samun nasarar zama gwamnan, kasancewar jam’iyyar tasa ce ta zo na biyu.

Alkalai bakwai karkashin jagorancin alkalin alkalan kasar, Mai shari’a Tanko Muhammad sun dage shari’ar bisa bukatar da lauyan APC Robert Clark ya gabatar kan bashi lokaci ya shigar da wasu sunayen da da kotun tayi kalubali akai, tare da yin bincike.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More