#ZabenEdo2020: Ta tabbata Obaseki na jam’iyyar PDP ne kan gaba a zaben Edo

Obaseki na kan gaba da akalla kuri’u  100,000 bayan sakamakon zaben kananan hukumomi 13

Gwamna Obaseki na jam’iyyar PDP  ne  a kan gaba a zaben gwamnan jahar Edo da aka gudanar  a  jiya Asabar, inda ake cigaba da  bayyana sakamakon  zaben.

Cibiyar tattara zaben INEC dake babban birnin jahar ta Edo, Benin city, ta tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 13 zuwa yanzu.

Obasaki na jam’iyyar  PDP  ya samu kuri’u 250,345, inda abokin hamayyar sa Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 154, 192 zuwa yanzu.

Jahar Edo tana da kanana hukumomi 18, kuma an kada kuri’u a dukkanin kananan hukumomin.

Ku kasance da #OakTVHausa dan samu labarai

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More