Zamfara:Sai Gwamnatocin jahohin sun hada karfi da karfe zamu kawo karshen yan bindiga – Gwamna Yari

Gwamnan jahar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce sai gwamnatocin jahohin da ke makwabtaka da jaharsa sun hada karfi da karfe  wajen yakar ‘yan bindiga da ke addabar al’ummar yankin kafin a samu nasara a kansu.

Ya bayyana hakan ne lokacin wata hira da ya yi da BBC a Abuja ranar Laraba 20 ga watan Maris 2019.

Jahar Zamfara na fara da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane ana karbar kudin fansa.

Gwamnan ya ce akwai bukatar a bai wa sojoji manyan bindigogi wajen yaki da mahara,saboda  karfin maharan bai yi kusa da na jami’an tsaron Najeriya ba.

Sojojin Najeriya suna da horo, suna da kayan aiki, suna da izini. Su kuma (‘yan bindigan) suna aiki ne na ta’addanci, dan haka  karfinsu ba zai zama daya ba.

Inda ya kara da cewa  maharan suna amfani ne da bindigogi “na al’ada” wato kanannan bindigogi, su kuma da jami’an tsaro suna amfani da manyan bindigogi saboda da haka wadannan manyan bindigogin muke so jami’an tsaro su fito su yi amfani da su dan cimma nasara akan yan bidiga dadin.

A karshe ya ce ya kamata sojoji su nuna wa maharan ba sani, ba sabo wajen yaki da su a duk lokacin da suka yi a aranga ma dasu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More