Zan samar wa yan Najeriya makoma ta gari a wa’adin mulki na na 2 – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi alkawarin yin bakin  kokarinsa wajen ganin ya kyautata wa dukkan yan Najeriya a karon mulkinsa na biyu. Ya kuma bayar da tabbacin cewa, zai yi aiki tukuru wajen  ganin ya samar wa Najeriya makoma ta gari tare da dukkan yan Najeriya, a yayin da ya fara zagaye wa’adin mulkinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayu 2019.

Sannan ya  mika godiya ga dukkan jama’ar da suka zabe shi a zaben da aka gudanar na ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu 2019.

Shugaba Buhari ya yi bayanin yayin da yake karbar bakoncin mambobin kwamitin amintattun kungiyar Gidauniyar Jahar Katsina (Katsina State Development Fund) karkashin jagorancin Maishari’a Mamman Nasir a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayyar Abuja.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, zagayen yakin neman zaben da ya yi a fadin tarayyar kasa ta Najeriya ya taimaka masa na sanin halin a kasar ke ciki.

A sanarwar da jami’in watsa labaransa Mista Femi Adesina ya sanya wa hannu, Buhari yan kuma bayyana cewa, ina matukar godiya a bisa goyon bayan da kuka bani, zan kuma yi bakin  kokarin a  zangon mulki na biyu wajen ganin  mu yi wa Najeriya da ‘yan Najeriya aiki yadda ya kamata.

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, jama’ar da suke halartar yakin neman zabensa a zagayen na biyu  sun fi karfin a ce ana basu kudi, ko kuma yaudarar su ake yi, ya ce wannan yana faruwa ne saboda yarda da amincewa da suke yi masa a kan mulkin da yake yi musu.

Shugaba Buhari ya kuma lura da cewa, shi ne shugaban gidauniyar Ilimi ta jahar Katsina na tsawon shekara 17, inda aka samu gaggarumin gudumawa a bangaren ilimi da harkar lafiya da aikin gona a fadin jahar, hakan yasa  talakawa suka amfana matuka.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More