Zanga-zangar Endsars: Wasu matasa sunyi wa gidan gwamnatin jahar Kogi shinge sun hana kowa shiga

Ana cigaba da zanga-zangar  Endsars duk da cewa babban sufeton ‘yansandan Najeriya Adamu Muhammad ya bayyana soke rundunar ta SARS inda kuma aka musanyata ta da rundunar ta SWAT.

Wasu matasai masu yawan da ka iya kaiwa 1000 sunyi tururuwa zuwa gidan gwamnatin jahar Kogi, inda suka  mata shinge, suka tsare haryar shiga cikin gidan gwamnatin suka hana kowa shiga ciki har da jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnatin jahar.

Rahotunni sun nuna cewa, matasan na cewa duk da soke rudunar ta SARS da shugaban ‘yansandan  Adamu Muhammad yayi, hakan  bazai hana su cigaba da gudanar da zanga-zangar su ba. Akwai bukatar sake yin gyara  akan lamarin na ‘yansandan Najeriya.

Duk da cewa  shugaban ma’aikatan na jahar ta Kogi, Jamiu Asuka, mai bawa gwamnatin shawara kan harkokin tsaro, Air Commodore Jerry Omodara da saura wasu manyan jami’an gwamnatin jahar sunyi kokari ganawa da su, sai dai matasan masu gudanar da  zanga-zangar sun bukaci ganin gwamnan jahar Yahaya Bello ne.

An cigaban da gudanar da zanga-zangar duk da cewa gwamnan  yayi gargadin a cikin jawabinsa, wanda ke cewa wasu ‘yan ta’adda sunyi kokarin ganin karshe rudunar ta SARS wacce aka kafata a shekarar 1992.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More