Zargi aikata laifi a Amurka: Kotu ta wanke Omo-Agege

Wata babbar kotun tarayya dake Bwari Abuja ta kori karar da aka shigar gabanta, na cewa ta sauke mataimakin shugaban majalisar dattawa  wato sanata Ovie Omo-Agege daga mukaminsa bisa zargin na cewa wata kotu ta taba yanke masa hukunci a Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ta rawaito  ce, mai Shari’a Othman Musa yana cewa karar  tana bata  lokacin kotu ne kawai domin kuwa babu wata kotu da ta taba daure shi a Amurka, sannan baya fuskantar wata shari’a a kasar.

A ranar laraba 29 ga watan Janairu ne, kotun ta  umarci wanda ya shigar da karar da ya biya Omo-Agege kudi naira miliyan 1 sakamakon bata masa suna daya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More