Zargin kai harin shaidun Atiku ba gaskiya bane – Yan sanda

Rundunar yan Sandan Najeriya reshen jahar Zamfara, sun karyata batun da kafafen watsa labarai suka ruwaito na cewar an kaiwa shaidun dan takarar shugaban kasa na  jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, hari a jahar ta Zamfara.

Alkalen Atiku sun shaidawa kotun sauraren kararrakin zabe na shugaban kasa a zaman karshe da aka yi cewa, an kaiwa shaidunsu hari a hanyarsu ta zuwa Abuja daga Zamfara.

Sai dai Kakakin yan Sandan Zamfara SP Muhammad Shehu, yar karyata zargin hakan , a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Gusau, inda  yace  ba su da labarin wannan hari a cikin jerin hare-haren da suka taskace a jahar.

Inda ya tabbatar da cewa, tun bayan zaman sulhu da Kwamishinan yan Sandan jahar Usman Nagogo, ya jagoranta da yan bindigar jahar, kashi 98 na  hare-hare yayi  saukin  a jahar ta Zamfara.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More