
Zidane: Hazard na da babbar matsala
Zinedine Zidane ya bayyana cewa Eden Hazard yana fama da wata matsala da ya dade yana dauke da ita.
Hazard ya sha suka a dan makonnin da suka gabata, inda wasu ke jayayya cewa bai mai da hankali akan wasan nin sa ba, amma shugaban Real Madrid yayi in karin wannan maganar.
“Ban yarda da hakan ba. amman Hazard yana so ya taka leda sosai,” in ji Zidane a lokacin taron manema labarai gabanin Talata.
“Yana da wata babbar matsala da ta dade tana damun shi.
“Lokacin yana da tsayi sosai kuma yana son kasancewa tare da abokan wasan sa.”