Zinadine Zidane ya yi watsi da tayin sake horas da Madrid

Zinadine Zidane ya yi watsi da tayin sake horas da Madrid, in ji tsohon shugaban Real Madrid Ramon Calderon

Zidane, mai shekaru 46, ya bar kulob din a kakar wasa ta bara, kwanaki Bihar kacal bayan ya jagoranci kungiyar ta lashe Gasar Zakarun Turai karo uku a jere.

Calderon ya shaidawa BBC 5 Alive cewa, ” na sani da safiyar nan, shugaba ( Florentino Perez) ya kira Zidane da ya dawo, amma ya ce ba yanzu ba.

” ya ba da kofar yiwuwar dawowarsa a watan Yuni.”

Real Madrid dai ta kadu da ajiye aikin Zidane, yan kwanaki kalilan da yin nasara akan Liverpool, wadda ta sa ya zama mai horaswa na farko da ya lashe gasar Zakarun Turai karo uku a jere.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More