Zuwan Buhari Umarah daraja ce ga Najeriya

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umarah yau Alhamis 2019
A wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar a shafinta na Twitter ranar Laraba, ta ce Sarki Salman Bin Abdulaziz ne ya gayyaci Buhari don gudanar da aikin.
Sanarwar ta bayyana cewa : “Shugaba Buhari ya amsa gayyatar da Sarki Salman Bin Abdulaziz ya yi masa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umarah a wannan watan mai falala, tare da masu taimaka masa na musamman.
“Ana sa ran zai komawar sa gida Najeriya a ranar Talata 21 ga watan Mayu 2019.

Mai bai wa shugaba Buhari shawara kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ”a idon duniya gayyatar Shugaba Buhari ya je ya yi Umarah, daraja ce da kima aka baiwa kasar Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More